06/09/2026
A ranar Asabar, 5 ga Satumba 2026, Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya ƙaddamar da shuwagabannin Door to Door Movement na ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina.
A Karamar Hukumar Bakori, Hon. Ibrahim Dan-Alkali ne zai jagoranci shirin.
Bayan kammala taron, Dan Alkalee Masari ya naɗa Ward Coordinators guda 11 Na Karamar Hukumar Bakori domin ƙarfafa tsarin ƙungiyar daga tushe da bunƙasa hulɗa da al’umma.
Muna taya waɗanda aka naɗa murna, tare da fatan za su sauke nauyin da aka ɗora musu cikin gaskiya, ƙwazo da kishin al’umma.
Allah Ya ba mu nasara, Ya sa mu wanye lafiya. Amiin.
Sun, 6th Sep, 2026.