APC MEDIA LEADS Katsina

APC MEDIA LEADS Katsina APC media leads kafar Watsa labarai Che ta zamani Wadda take Tallata Aiyyukan Gwamnatochin Yan Jam,iyyar Apc tun daga Shugaban kasa har zuwa kansila.

22/08/2026

Alhamdulillah Alhamdulillahi Alhamdulillah
Godiya ta tabbata ga Allah
Ofishin Apc media leads ya fara daukar harami sunayen wadanda s**a bamu gudummuwa na nan tafe Dana wadanda s**a dauki Alkawalin badawa.

Alhamdulillah lillahi wannan kungiya mai suna APC MEDIA LEADS Katsina ta chika Alkawalin da ta dauka na sanya ma mutane ...
21/08/2026

Alhamdulillah lillahi wannan kungiya mai suna APC MEDIA LEADS Katsina ta chika Alkawalin da ta dauka na sanya ma mutane 20 data wadanda s**a hada Hoton Gwamna raddda da logon kungiyar ba tare da samun wata matsala ba ko daukar na wani ka turo

Makasudin wannan kyautar data domin sada zumunchi tare da matsa siyasa
Muna Taya wadanda s**a samu murna wadanda basu samu ba muna basu hakuri zuwa wata nagaba da izinin Allah mun fara kenan

Mungode Kwarai da zumunchi da muka sada domin amfanin wannan Giveway kenan ba don samun data ba sai don sada zumunchi Allah ya Kara hada kan yan media jihar katsina wata rana mu fiddo wani chikin mu yayi takarar Gwamna muna. Fatan Allah ya kawo mamu wannan ranar Ameen,

Gwamna Radda Ya Nada Al-amin Batsari a Matsayin SSA a KASEDAMaigirma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph....
21/08/2026

Gwamna Radda Ya Nada Al-amin Batsari a Matsayin SSA a KASEDA

Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., ya nada Al-amin Batsari a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (SSA) a Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Katsina (KASEDA).

Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka wajen ƙarfafa ƙananan da matsakaitan sana’o’i da kuma bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar.

GIVEAWAYS! GIVEAWAY!! GIVEAWAYS!!!More gara basar samun Data daga APC MEDIA LEADS Katsina, dauki wannan hoton ka hada da...
21/08/2026

GIVEAWAYS! GIVEAWAY!! GIVEAWAYS!!!

More gara basar samun Data daga APC MEDIA LEADS Katsina, dauki wannan hoton ka hada da hoton mai girma gwamna Dikko Radda ka rubuta Falle biyuce a baya ka sanya mana a comment section tare da number wayar ka.

21/08/2026

Sarkin wakar kasar Hausa fah sai an jira Dauda Kahutu Rarara

Shugaba Tinubu Ya Baiwa Kowane Ɗalibi Damar Karatu, Ya Kamata Ɗalibai Su Maida Biki — Gwamna RaddaGwamnan Jihar Katsina,...
20/08/2026

Shugaba Tinubu Ya Baiwa Kowane Ɗalibi Damar Karatu, Ya Kamata Ɗalibai Su Maida Biki — Gwamna Radda

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa tsarin rancen karatu na NELFUND da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samar, ya baiwa kowane ɗalibi damar zuwa makaranta ba tare da la’akari da halin tattalin arzikinsa ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa reshen arewa maso yamma "National Association of Nigerian Students (NANS), Zone A", waɗanda s**a gudanar da tattaki domin nuna goyon bayansu ga Shugaba Tinubu da Gwamna Radda a zaɓen 2027.

Sakataren ƙungiyar wanda yake wakiltar shiyyar Arewa maso Yamma , Kwamared Lawal Isa Federal, ya bayyana cewa irin ci gaban da Gwamna Radda ya kawo a fannin ilimi ne ya sa ɗaliban s**a amince da sake ba shi dama, musamman biyan tallafin karatu, samar da guraben karatu a ƙasashen waje, kafa makarantu na musamman, ginawa da gyaran makarantun firamare da sakandare.

Gwamna Radda ya ce ya kamata ɗalibai su maida irin wannan ci gaba abin murna, musamman tsarin da shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu ya kawo na NELFUND, wanda ya baiwa ɗalibai damar samun ilimi ko da ba su da isasshen ƙarfin kuɗi.

Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Taimakawa Gwamnan Jihar Katsina kan Harkokin Ɗalibai, Hon. Muhammad Nagaske.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

August 20, 2026.

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina,Rt.Hon Aminu Bello Masari ya gana da masu riƙe da mukaman siyasa na Gwamnatin Tarayya, waɗa...
20/08/2026

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina,Rt.Hon Aminu Bello Masari ya gana da masu riƙe da mukaman siyasa na Gwamnatin Tarayya, waɗanda Mai Girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa, a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina da ke Asokoro,Abuja.

A yayin ganawar, an tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi ci gaban Jihar Katsina, haɗin kai da kuma yadda za a ƙara ƙarfafa goyon bayan al’umma ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. Da Gwamna Jahar Katsina Dr Dikko Radda PhD

Ku Rabu da Duk Wani Ƙage da Wasu Mutane Ke Yunkurin Yaɗawa Dangane da APC Media Leads Katsina!APC Media Leads Katsina ƙu...
20/08/2026

Ku Rabu da Duk Wani Ƙage da Wasu Mutane Ke Yunkurin Yaɗawa Dangane da APC Media Leads Katsina!

APC Media Leads Katsina ƙungiya ce da aka kafa domin tallata manufofi da ayyukan alheri na Jam’iyyar APC, tare da yaɗa ayyukan shugabannin jam’iyyar daga matakin Shugaban Ƙasa har zuwa matakin Kansila.

APC Media Leads ta kowa ce, kuma ta ‘ya’yan APC baki ɗaya ce.

Abin takaici ne yadda wasu ke ƙoƙarin haifar da rashin fahimta tsakanin wannan ƙungiya da wasu ‘yan takara. Ya kamata a fahimci cewa APC Media Leads ba ta ware kanta ga wani mutum ɗaya ba; ƙungiya ce ta ‘ya’yan APC, kuma tana tare da duk wanda ke aiki domin ci gaban jam’iyyar.

APC Media Leads za ta ci gaba da tallata APC da ayyukan shugabanninta daga sama har ƙasa, Insha Allahu.

🇳🇬 Najeriya Sai Tinubu! ✅
💚 Katsina Sai Dikko! ✅
💪 Katsina Zone: Audu Soja! ✅
🔥 Katsina Central: Abba Mangal! ✅
💪 Katsina Local Government: Aliyu Albaba! ✅

Allah Ya ba Jam’iyyar APC nasara. Amin. 🤲

We are ready to go...
20/08/2026

We are ready to go...

Address

No 155 Nagogo Road Kofar Durbi Katsina
Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when APC MEDIA LEADS Katsina posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share