07/09/2026
RAHOTON ƘARSHE NA KWAMITIN HAƊIN GWIWA DA KYAUTATA ALAƘAR WAJE
BIKIN SANA’O’IN HANNU NA KATSINA (1.0)
Zuwa:
Kwamitin Ƙasa/Masu Shirya Bikin Sana’o’in Hannu na Katsina (1.0)
Daga:
Kwamitin Haɗin Gwiwa da Kyautata Alaƙar Waje
Kwanan Wata:
7 ga Satumba, 2026
Maudu’i: RAHOTON ƘARSHE NA AYYUKAN KWAMITIN, GODIYA DA RUSHEWAR KWAMITIN
1.0 GABATARWA
Kwamitin Haɗin Gwiwa da Kyautata Alaƙar Waje na Bikin Sana’o’in Hannu na Katsina (1.0) na gabatar da wannan rahoto na ƙarshe domin sanar da Kwamitin Ƙasa/Masu Shirya Biki game da ayyukan da kwamitin ya gudanar tun bayan kafa shi a ranar 15 ga Yuli, 2026, da kuma yadda ya cika wa’adin aikin da aka ɗora masa.
An kafa kwamitin ne da manufar tuntuɓar hukumomin gwamnati, ma’aikatun gwamnati, hukumomi da hukumomin gwamnati (MDAs), cibiyoyin kuɗi, kafafen yaɗa labarai, ƙungiyoyin sana’o’i, cibiyoyin ilimi, ƙungiyoyin matasa, kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki, domin samar da hanyoyin haɗin gwiwa da tallafa wa nasarar gudanar da Bikin Sana’o’in Hannu na Katsina (1.0).
Wa’adin farko na kwamitin ya kasance daga 15 ga Yuli zuwa 31 ga Yuli, 2026. Bisa muhimmancin ayyukan da aka fara da kuma buƙatar cigaba da tuntuɓar abokan hulɗa, an tsawaita wa’adin kwamitin. Wannan ƙarin lokaci ya ba kwamitin damar kammala wasu muhimman ayyuka tare da gabatar da sakamakon ayyukansa a Taron Manema Labarai da aka gudanar a ranar Lahadi, 6 ga Satumba, 2026.
Bisa haka, kwamitin ya ɗauki wannan ranar a matsayin ranar kammala aikin da aka ɗora masa.
2.0 AYYUKAN DA KWAMITIN YA GUDANAR
A lokacin aikinsa, kwamitin ya gudanar da tuntuɓa, ziyara, tattaunawa da musayar ra’ayi da wasu muhimman hukumomi, cibiyoyi da ƙungiyoyi domin neman haɗin gwiwa da goyon baya ga bikin.
Daga cikin waɗanda aka tuntuɓa akwai:
1. Hukumar Bunƙasa Fitar da Kayayyakin Najeriya (NEPC) – Ofishin Jihar Katsina
2. Hukumar Kula da Rajistar Sha’anin Ɗan Adam ta Ƙasa (NIMC) – Ofishin Jihar Katsina
3. Shugabannin Ƙungiyoyin Sana’o’i da Ƙungiyoyin Masu Ruwa da Tsaki
4. Katsina State Television Service (KTTV)
5. Katsina State Radio Service
6. Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta Jihar Katsina (KIPA)
7. Gram FM Katsina
8. Moniepoint Microfinance Bank Ltd. – Ofishin Katsina
9. Hukumar Kula da Kimiyya da Ilimin Fasaha ta Jihar Katsina
10. Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Katsina
11. First City Monument Bank (FCMB) – Reshen Katsina
12. Jaiz Bank PLC – Reshen Katsina
13. Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar Katsina
14. Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidimar Ƙasa (NYSC) – Ofishin Jihar Katsina
15. Majalisar Bincike da Bunƙasa Albarkatun Ƙasa (RMRDC) – Ofishin Jihar Katsina
16. Department of Fine and Applied Arts, Federal College of Education, Katsina
17. Department of Hausa, Federal College of Education, Katsina
18. Amalgamated Youth Entrepreneurs Development Cooperative Union (KAYEDCU)
19. Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA)
20. Hukumar Kula da Tarihi da Raya Al'adu ta Jihar Katsina.
Waɗannan tuntuɓe - tuntuɓe sun taimaka wajen samar da ƙarin fahimta game da irin gudunmawar da hukumomi, cibiyoyi da ƙungiyoyi daban-daban za su iya bayarwa wajen bunƙasa sana’o’in hannu da kuma gudanar da bikin cikin nasara.
3.0 MANYAN FANNONIN HAƊIN GWIWAR DA AKA TATTAUNA
A yayin tuntuɓar masu ruwa da tsaki, an fi mayar da hankali kan hanyoyin da za a iya samun haɗin gwiwa a fannoni kamar:
- Tallata da haɗa kayayyakin sana’o’in hannu da kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje;
- Samar da dama ga masu sana’a wajen samun kasuwa;
- Rajista da tattara bayanan masu sana’o’in hannu;
- Hada masu sana’a da cibiyoyin kuɗi da hanyoyin samun jari;
- Horas da matasa da mata kan sana’o’in hannu da dabarun kasuwanci;
- Haɗa sana’o’in hannu da ilimi da bincike;
- Samar da damar amfani da fasaha wajen ƙera da tallata kayayyaki;
- Wayar da kan jama’a ta kafafen yaɗa labarai;
- Samar da hanyoyin sufuri da sauƙaƙe zirga-zirgar kayayyaki;
- Bunƙasa zuba jari a harkar sana’o’in hannu;
- Haɗa sana’o’in hannu da aikin gona da sarrafa amfanin gona;
- Ƙarfafa matasa da ƙungiyoyin ’yan kasuwa su shiga harkar sana’o’i;
- Samar da haɗin gwiwa tsakanin masu sana’a, cibiyoyin ilimi, hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
4.0 SAKAMAKON TUNTUƁA
Kwamitin ya samu kyakkyawar tarba daga mafi yawan hukumomi, cibiyoyi da ƙungiyoyin da aka tuntuɓa. Wasu daga cikinsu sun nuna sha’awar yin aiki tare da shirin, yayin da wasu s**a buɗe ƙofofin tattaunawa domin duba hanyoyin da za su iya bayar da gudunmawarsu.
Kwamitin ya kuma fahimci cewa tuntuɓar masu ruwa-da-tsaki ba ta tsaya ga lokacin shirye-shiryen bikin kawai ba. A maimakon haka, alaƙoƙin da aka kafa na iya zama tushen samar da dogon zango na haɗin gwiwa domin cigaban sana’o’in hannu, ƙananan ’yan kasuwa, matasa da sauran masu ruwa-da-tsaki a Katsina.
Saboda haka, ana ba da shawarar cewa Kwamitin Ƙasa/Masu Shirya Biki su cigaba da bibiyar waɗannan alaƙoƙi tare da mayar da su cikin tsari na aiki bayan kafa kwamitin da zai jagoranci shirye-shiryen gudanar da bikin.
5.0 GODIYA
Kwamitin Haɗin Gwiwa da Kyautata Alaƙar Waje yana amfani da wannan dama wajen bayyana godiya ta musamman ga Kwamitin Ƙasa/Masu Shirya Bikin Sana’o’in Hannu na Katsina (1.0) bisa amincewa da aka yi da shi, da kuma damar da aka ba shi na taka rawa wajen wannan muhimmin shiri.
Muna kuma miƙa godiyarmu ga dukkan hukumomin gwamnati, ma’aikatun gwamnati, cibiyoyin kuɗi, kafafen yaɗa labarai, cibiyoyin ilimi, ƙungiyoyin sana’o’i, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki da s**a karɓi wakilan kwamitin hannu biyu-biyu, s**a saurare su, s**a ba da shawarwari tare da nuna sha’awar haɗa kai da Bikin Sana’o’in Hannu na Katsina (1.0).
Musamman, muna godiya ga dukkan waɗanda aka tuntuɓa domin ba da lokaci, shawarwari da goyon baya wajen fahimtar manufofin bikin.
Muna kuma yaba wa dukkan mambobin kwamitin bisa sadaukar da lokacinsu, jajircewarsu da haɗin kan da s**a nuna a duk tsawon lokacin da s**a gudanar da wannan aiki.
6.0 KAMMALA AIKIN KWAMITIN
Bisa cikar wa’adin da aka ƙara wa Kwamitin Haɗin Gwiwa da Kyautata Alaƙar Waje, da kuma kammala ayyukan da aka ɗora masa, musamman gabatar da rahoton ayyukansa a Taron Manema Labarai na ranar Lahadi, 6 ga Satumba, 2026, kwamitin yana sanar da cewa ya kammala aikinsa a hukumance.
Saboda haka, daga ranar 6 ga Satumba, 2026, za a ɗauki aikin wannan kwamiti a matsayin wanda aka kammala, kuma kwamitin ya miƙa duk wani bayani, bayanan tuntuɓa da shawarwarin da aka samu ga Kwamitin Ƙasa/Masu Shirya Biki domin cigaba da amfani da su wajen shirye-shiryen bikin.
Wannan ba yana nufin an kawo ƙarshen dangantakar da aka kafa tsakanin bikin da masu ruwa-da-tsaki ba ne; a maimakon haka, an kammala aikin kwamitin ne domin a ba da damar shiga mataki na gaba na shirye-shiryen gudanar da bikin.
7.0 SABON TSARIN SHIRYE-SHIRYEN GUDANAR DA BIKI
Bayan kammala aikin Kwamitin Haɗin Gwiwa da Kyautata Alaƙar Waje, Building Your Future Ambassadors' Initiative (BYFAI), ƙarƙashin jagorancin Steering Committee, za ta kafa wani sabon kwamiti na musamman mai suna:
KWAMITIN SHIRYE-SHIRYEN GUDANAR DA BIKIN SANA’O’IN HANNU NA KATSINA (1.0)
Wannan sabon kwamiti zai mayar da hankali kai tsaye kan shirye-shiryen gudanar da bikin, da s**a haɗa da tsara jadawalin ayyuka, wuraren gudanar da taruka, kula da mahalarta, shirya tarukan baje koli, hulɗa da masu gabatar da shirye-shirye, kula da kayan aiki, tsaro, sufuri, kafafen yaɗa labarai, baƙi na musamman da sauran muhimman abubuwan da s**a shafi gudanar da bikin.
Za a sanar da tsarin mambobin sabon kwamitin da nauyin da aka ɗora wa kowane sashe bayan amincewa da shi daga Steering Committee na BYFAI.
Ana sa ran wannan sabon tsarin zai tabbatar da cewa an samu kyakkyawan sauyi daga matakin tuntuɓar masu ruwa-da-tsaki da gina alaƙa zuwa matakin shirye-shiryen gudanar da bikin kai tsaye.
8.0 SHAWARA
Kwamitin yana ba da shawarar cewa dukkan alaƙoƙin da aka fara kafawa da hukumomi, cibiyoyi da ƙungiyoyi su cigaba da kasancewa cikin ƙudirin sabon Kwamitin Shirye-shiryen Gudanar da Bikin, domin kada ƙoƙarin da aka yi ya tsaya bayan kammala aikin wannan kwamiti.
Haka kuma, ana ba da shawarar a cigaba da bibiyar waɗanda s**a nuna sha’awar haɗin gwiwa domin tabbatar da cewa sha’awar ta koma zuwa haƙiƙanin haɗin gwiwa da gudunmawa a lokacin gudanar da Bikin Sana’o’in Hannu na Katsina (1.0).
9.0 KAMMALAWA
Kwamitin Haɗin Gwiwa da Kyautata Alaƙar Waje na alfahari da damar da aka ba shi na yi wa Bikin Sana’o’in Hannu na Katsina (1.0) hidima.
Muna fatan cewa ƙoƙarin da aka yi wajen gina alaƙa da masu ruwa-da-tsaki zai zama ginshiƙi mai ƙarfi wajen samun nasarar wannan biki da kuma samar da ɗorewar haɗin gwiwa bayan kammala bikin.
Muna addu’ar Allah Ya sa Bikin Sana’o’in Hannu na Katsina (1.0) ya kasance wata muhimmiyar kafa wajen bunƙasa sana’o’in hannu, ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci da tattalin arziƙin al’umma a Katsina da Arewa baki ɗaya.
Allah Ya sa a dace.
Sa hannu:
Mubarak Saleh Bakiyawa
Sakatare
Kwamitin Haɗin Gwiwa da Kyautata Alaƙar Waje
Bikin Sana’o’in Hannu na Katsina (1.0)
7 ga Satumba, 2026
25 ga Rabi'ul-Awwal, 1448