05/09/2026
SANARWAR Taron Manema Labarai
Kwamitin Haɗin Gwiwa da Kyautata Alaƙar Waje na Bikin Sana’o’in Hannu na Farko na Jihar Katsina (Katsina Crafts Festival 2026) na farin cikin gayyatar ’yan jarida, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkar sadarwa zuwa wani muhimmin taron ganawa da manema labarai.
Taron zai kasance wata dama ta musamman domin bayyana wa jama’a manufofi, shirye-shirye da muhimmancin Bikin Sana’o’in Hannu na Farko na Jihar Katsina, wanda ke da taken:
“Unlocking Katsina’s Creative Economy”
(Buɗe Ƙofofin Tattalin Arziƙin Ƙirƙira na Katsina).
Taron zai kuma mayar da hankali kan yadda za a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu sana’o’in hannu, masu fasaha, gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu, masu zuba jari da kafafen yaɗa labarai, domin bunƙasa harkar sana’o’i da ƙirƙire-ƙirƙire a Jihar Katsina.
BAYANAN TARON
📅 Rana: Lahadi, 6 ga Satumba, 2026
⏰ Lokaci: 10:00 na safe daidai
📍 Wuri: NUJ Secretariat, Old KTTV Road, Katsina City, Katsina State.
Taron zai kasance ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa da Kyautata Alaƙar Waje na Bikin, kuma Darakta Janar na Building Your Future Ambassadors’ Initiative (BYFAI), Dr. Isah Rabe Kambarawa, CPM, CPD, CHRM.
Muna kira ga ’yan jarida da dukkan kafafen yaɗa labarai da su kasance cikin wannan muhimmin taro, domin tare za mu iya tallata al’adun Katsina, sana’o’in gargajiya, fasaha da damar da tattalin arziƙin ƙirƙire-ƙirƙire ke da ita wajen samar da guraben ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziƙin Katsina State Government ƙarƙashin jagorancin Shugaba Mai Hangen Nesa Malam Dr. Dikko Umaru Radda, PhD, CON.
Katsina Crafts Festival 2026 - Mu buɗe ƙofofin tattalin arziƙin ƙirƙire-ƙirƙire tare.