21/10/2024
Hon. Muzammil Muhammad Idris ya sayi fom din takarar shugabancin karamar hukumar Kaura Namoda, kuma ya cike dukkan sharudda kamar yadda doka ta tanada, ya cike fom din sannan y mayar kamar yadda doka ta tanadar. Wannan mataki yana nuna kudurinsa na kawo ci gaba ga al'ummarsa tare da inganta rayuwar mutanen yankin. Idan aka ba shi dama, Hon. Muzammil zai yi amfani da gogewarsa wajen inganta manyan bangarorin ci gaba guda shida, wato:
1. Inganta Ilimi.
2. Inganta lafiyar al'umma.
3. Inganta wutar lantarki.
4. Samar da hanyoyin dogaro da kai da inganta tattalin arziki.
5. Bunkasa Noma.
6. Inganta tsaro.