Kaura Namoda city

Kaura Namoda city Kaura Namoda Zamfara State Nigeria.

24/07/2026

Alhamdulillah
Cikin ikon Allah yau wani bawan Allah ya musulunta a masallacin jumu'a na farko, kuma ya rabauta da suna BILYAMINU.

Alh Ibrahim Galadima wanda Allah yayima rasuwa a jiya, yana samun yabo da shedar tausayawa zuwa ga marasa lafiya musamma...
28/06/2026

Alh Ibrahim Galadima wanda Allah yayima rasuwa a jiya, yana samun yabo da shedar tausayawa zuwa ga marasa lafiya musamman yara kanana.

Allah kayi mashi rahama yasa aljanna ce makomarsa tareda uwayenmu baki daya Ameen.

Illolin Zina Guda Ashirin (20)1. Zina tana jawo fushin Allah Maɗaukaki.2. Tana rage albarka a rayuwa da arziki.3. Tana l...
24/06/2026

Illolin Zina Guda Ashirin (20)

1. Zina tana jawo fushin Allah Maɗaukaki.
2. Tana rage albarka a rayuwa da arziki.
3. Tana lalata tarbiyyar mutum da mutuncinsa.
4. Tana jawo kunyata a duniya da lahira.
5. Tana raunana imani da tsoron Allah.
6. Tana haifar da yawaitar rabuwar aure.
7. Tana rushe amana tsakanin ma’aurata.
8. Tana haddasa rikice-rikicen iyali.
9. Tana jawo yaɗuwar cututtuka masu haɗari.
10. Tana haifar da ɗaukar ciki ba tare da aure ba.
11. Tana haddasa zubar da ciki da kashe rayuka.
12. Tana jawo rikicin nasaba da rashin sanin uba.
13. Tana lalata tarbiyyar yara da makomar al’umma.
14. Tana jawo damuwa, nadama da tashin hankali.
15. Tana rage ƙima da darajar mutum a idon jama’a.
16. Tana iya kai mutum ga talauci saboda kashe dukiya a haram.
17. Tana buɗe ƙofofin wasu zunubai kamar ƙarya da yaudara.
18. Tana karya zaman lafiya da kwanciyar hankali a al’umma.
19. Tana hana karɓuwar wasu ibadu idan ba a tuba ba.
20. Tana jawo azaba mai tsanani idan mutum bai tuba ba.

Allah Ya ce:

﴿وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَىٰ ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا﴾

“Kada ku kusanci zina; lallai ita alfasha ce kuma mummunar hanya ce.”
— Al-Qur’ani Mai Girma

Allah Ya tsare mu daga zina da duk hanyoyin da ke kaiwa gare ta, Ya kuma azurta mu da tsarki da kamun kai. Ameen.

Innalillahi Wa'inna Ilaihirrajiun.Muna jajantama ma'aikatan makarantar Federal Polytechnic kaura namoda da dalibanta aka...
23/06/2026

Innalillahi Wa'inna Ilaihirrajiun.

Muna jajantama ma'aikatan makarantar Federal Polytechnic kaura namoda da dalibanta akan rasuwar tsohon ma'aikaci kuma popular staff Malan BaBa Sada, Ubangiji Allah yayi masa rahama yasa aljanna ce makomarsa tareda uwayenmu baki daya.

Tawagar Uban Musulmai.Allah ya kara maka daraja da martaba a idon duniya.
12/06/2026

Tawagar Uban Musulmai.

Allah ya kara maka daraja da martaba a idon duniya.

08/06/2026

Yau nasamu labarin wani driver da akayi kidnapped har sau 6 ana biyan kudin fansa a sakoshi.

07/06/2026

Allah ya kaimu gobe lafiya.

07/06/2026

Allah gatan bayinsa😭

Address

Kaura-Namoda

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kaura Namoda city posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share