04/08/2026
Bismillāhir Raḥmānir Raḥīm
Ya Allah, Mai iko a kan komai, Mai ba da nasara ga wanda Ka so, muna roƙonKa Ka rubuta mana nasara a rayuwarmu; nasara mai albarka, mai ɗorewa, wadda za ta kusantar da mu zuwa gare Ka.
Ya Rabbana, Ka tsarkake niyyarmu, Ka gyara zukatanmu, Ka shiryar da mu zuwa ga hanya madaidaiciya. Ka ba mu ilimi mai anfani, da fahimta mai zurfi, da hikimar da za mu yi amfani da ita cikin adalci da gaskiya.
Ya Allah, Ka buɗe mana ƙofofin alheri daga inda ba mu yi zato ba. Ka sauƙaƙa mana wahalhalu, Ka ba mu juriyar fuskantar ƙalubale, Ka sa mu kasance cikin masu tawakkali gare Ka a kowanne hali.
Ya Fattāḥu, Ka buɗe mana ƙofofin nasara.
Ya Razzaq, Ka azurta mu da halal mai yalwa.
Ya Latīf, Ka sauƙaƙa mana al’amuranmu.
Ya Naṣīr, Ka taimake mu kan abin da ya gagare mu.
Ya Allah, Ka sa nasararmu ta kasance tare da tawali’u, ba tare da girman kai ba; tare da godiya, ba tare da mantuwa ba; tare da amfani ga addininmu da iyalanmu da al’ummarmu.
Rabbana ātinā fid-dunyā ḥasanah, wa fil-ākhirati ḥasanah, wa qinā ‘adhāban-nār.
Āmīn Yā Rabbal-‘Ālamīn. 🤲
✍️ Comrade Garba Sani Muhammad