28/02/2026
*TARIHIN KOFOFIN GARIN KAZAURE*
*Shimfida*
Kamar yadda muka sani cewa duk inda aka samu kofar gari toh tabbas zaāa samu Ganuwa wadda take kewaye da wadanan kofofin.
Wannan haka yake a garin Kazaure ma domin kuwa akwai ganuwar data kewaye garin Kazaure.
Asali dai dukkan garin daāaka samu ganuwa wannan yana nuna cewa garin tsohon garine, kuma yana nuna cewa wannan garin ya gwabza yaki daban daban.
1. Akwai kofofin Gari guda sida (6) a garin Kazaure.
1. kofar Gabas
2. ā Kofar Yamma
3. ā Kofar Arewa
4. ā Kofar Kudu
5. ā kofar Rairayi
6. ā kofar Yarimawa
Wadannan sune manyan kofofin daāake dasu a gari Kazaure.
2. Asalin wadannan kofofi an ginasune tun farkon Karni na 19 a zamanin Sarkin Kazaure Dambo. k**ar yadda yake a tarihi cewa bayan da sarkin musulmi Muhammadu Bello Dan Shehu yayi sulhu tsakanin Sarkin Kazaure Mal. Dantunku da Sarki Kano Mal. Dabo da kuma haramta yaki tsakaninsu. Sai Sarki Malam Dantunku yanemi izini Sarkin Musulmi domin ya gina gidan Sarauta, Masallaci da kuma Ganuwar garin Kazaure.
Bayan da Sarkin musulmi yabada izinin sai aka k**a wadancan ayyukan ( zamuyi cikakkan bayani idan munzo magana akan gidan Sarkin Kazaure). Kodayake an fara wani bangare na aikin a lokacin Mal. Dantunku yana raye saidai an k**alla ayukan baki daya a zamanin Sarki Dambo bayan rauswar Mal. Dantunku.
3. Saboda haka Sarki Dambo ne yafara gina ganuwar Kazaure tare da ginamata kofofin shiga gari.
4. Wadancan kofofin sun samu sauyi wajen dasuke har sau kusan ukku.
a. Da farko an gina ganuwar garin Kazaure tare da gina kofofin guda biyar (5) watau kofar Gabas, Kofar Yamma, Kofar Kudu, kofar Arewa, Kofar Yarimawa.
Ga guraben kofofin a lokacinda aka fara ginasu
i. Kofar Gabas: kofar gabas an ginatane a daidai tudun dazaāa gangara gidan Dan iya watau gaban tsohuwar works ko muce gidan yan kwana-kwana.
ii. kofar Arewa : Da farko an ginata daidai kant**in Tsohon Kafi daidai gida Marigayi Sarki Fulanin Jawo Alh. Sani Doctor.
iii. Kofar Yarimawa : ita wannan Kofar itace take a wajen gaganren dam.
iv. kofar Kudu: kofar kudu itama bata samu chanji wajen ba . Tana inda aka ginata tun farko kafin ta tashi.
v. kofar Yamma: ita kofar yamma asalinta an ginatane a daidai tudun wayo watau wajejen gida Marigayi Alh. Ibrahim Maāaji Matawallen Kazaure.
*Fadada Ginin Ganuwar Gari da Sauyawa Kofofi Wuri*
*Kofar Arewa*
Bayan da aka gina ganuwar gari ta farko zamanin Sarki Dambo sai kuma Sarki Dambo ya fadada Ganuwar gari daga Arewa inda aka shigar da unguwar Tsohon Kafi cikin ganuwar garin Kazaure. Wannan aikin anyishine bada jimawa ba bayan gina waccan ganuwar ta farko. A saboda wannan aikine yasa kofar garin Arewa ta tashi daga inda take ta koma wajen datake a yanzu. A cikin shekarar 1988 Tsohon Shugaban karamar Hukumar Kazaure marigayi Alh. Aminu Umar ya sake ginata akan yanayin ginin zamani wanda shine ya kasance har izuwa yanzu.
*Kofar Gabas*
A zamanin Sarki Kazaure Mal. Muhammadu Bello (1882-1914) Mayaki ne, Sarki Mayaki ya kara fadada Ganuwar Garin Kazaure ta Gabas da kuma gabas maso Kudu inda wannan ne yasa Kofar Gabas ta tashi daga wajen daāaka fara ginata ta koma gurbin datake kafin a rusheta. A cikin shekarar 1988 Tsohon Shugaban karamar Hukumar Kazaure marigayi Alh. Aminu Umar ya sake ginata akan yanayin ginin zamani wanda shine ya kasance har aka rusheta a yan shekarun baya saboda aikin t**i.
*Kofar Yamma*
Kofar yamma itama ta samu canji waje a lokacin daāaka shigar da unguwar Ganuguli ( wadda aka zagayewa Mal. Muhammadu Ganguli tun zamanin Sarki Dantuku wanda saboda sunanshine unguwar ta samo sunanta na Unguwar Ganguli) zamuyi bayani akan wannan unguwa insha Allah). Wannan aiki anyishine a zamanin Sarki Mayaki. Saboda wannan daliline aka dauke waccan kofar daga wajen daāaka ginata na asali inda ta koma unguwar Ganguli ( Birnin Ruwa) sak**akon fadada badalar gari da shigo da Unguwar Ganguli cikin badala. ( asalin kofar tana wurin daāake kira Birnin Ruwa kusan yanzu wajen yana cikin dam). Daga bisani Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kazaure Marigayi Alh. Lawan Shehu Dan Amar din Kazaure (???) ya gyarata ta koma ta zamani. Kana daga bisani a cikin shekarar 2022 Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kazaure Hon. Muhammad Muktar Zannan Kazaure ya gina sabuwar kofar yamma a gurbin wadda aka rushe kuma aka sanyamata suna Kofar Sarki Dambo.
Wannan shine takaitaccen bayani akan kofifin garin Kazaure. Sauran bayanai zasuzo anan gaba. Da kuma wanda zaizo a cikakkaen rubutun tarihin Masarautar Kazaure.
Wannan shafi yana maraba da karin haske, gyara ko tsokaci.
Allah ya jikan magabantanmu.
Alk**alu Lillahi.
Wakilin Tarihi ( WT)