09/08/2014
ALUSHA
fitowar farko 1
daga taskar m abdul
Allahu akbar masu iya magana s**a ce "sabo dayi gawa da gatsine"ALUSHA Dai yana chan yakasa tsaye ya kasa zaune yana ta neman wata hanyar da za asamu wata abokiyar rayuwa,ana nan cikin haka wata rana sai ya kai wa abokinsa AMIL ziyara s**a fito da benci s**a zauna suna hira,chan sai ga wasu yan mata guda uku sun jero daya bayan daya za su shige.koda yan matan nan s**a kusa zuwa daf da su,sai Alusha yace kai Amil gaba ko baya ko tsakiya?sai shi kw yace wai ai duk cikinsu bb ta yarwa inda zasu samu. Su kuwa yan matan sai s**a yi kunnan uwar shegu kamar basu ji abinda s**a fada ba.
Bayan yan matan sun sake dawowa zasu wuce,sai Alusha ya ce da Amil 'kai arashn tayi fa ake barin araha 'Amil sai yayi murmushi ya ce ,a wajen km tayi ake mutum yake zurma kansa ba,ALUSHA yace E,naji ni dai sai na dan latsa ko zata kai min .da isowar yan matan sai Alusha ya yi wuf da sauri ya tashi ya sha gabansu ya ce, wai ku wace irn zirga zirga kk mana anan ne?in bata kky ai sai kuyi magana asa ku ahanya ko?sai karamar ciknsu ta tsaya su kuma sauran s**a wuce ta kalle shi kasa da sama tace,kai kuma waye kai gadin wannan hanyar aka baka ne ko kuwa?kafin ya buda baki ya bata amsa sai sauran yan matan da s**a wuce s**a ce 'don Allah Aliya ki manta da shi ki zo mu tafi. Bala ne.
Shi kuma Amil da jin sun fadi sunanta, sai ya taso ya ce. 'ai kuwa abin ya dace ,ke Aliya shi km Alusha.ita kuma data ji haka.kaunarsa sai ta shga ranta ta dan fara yin murmushi tana kallonsa,kallo na hakika ta ga babu shakka duk inda kyakkyawan saurayi yake shi ma ya kai, sai tace don Allah daga yau ku dinga sanin wadanda za ku dinga tarewa .amma yanzu kaci albarkacin sunan naka. Ba don haka ba, da ko kah waye sai nasa anci mutuncinka yadda gobe in ka ga wasu yan mata baza ka sake sha awar tare su ba, Alusha ya ce to na gode , amma zancen cewa zaki sa wai aci min mutunci da kk fada,ai ko ke ce yar sakin garin nan wato M abdul to a wannan lokaci dana ganku ba zan iya rabuwa da ku bance komai ba.musanman akanki don a hakikanin gaskiya a yadda na ganki din nan a ce ayau banji muryarki ba,to ban san yadda zanyi na rarrashi zuciyata har ta iya mantawa da ke ba. Kuma a halin yanzu ma koda zaki sa a soke ni, ni dai bukatata ta biya, tun da ban bar zuciya ta acikin bakin ciki ba,
ita kuma da ta ji ya fadi haka, sai tayi sauri ta hada fuskarta kamar ranta ya baci ta ce, to shike nan ka saurari abinda zai biyo baya. Sai ta juya zata tafi sai ya yi sauri ya rike mayafinta ya sake cewa.........
Kasance tare dani dan jin karshen lbrn..