15/10/2021
TSARABAR JUMA'A...
Allah duk alkhairin da ke tattare da wannan ranar mai tarin albarka, Allah ka kawo manashi, Akasin hakan kuma ka kare mu dashi. Amin👏🏻👏🏻👏🏻
Yaa Allah 'Yan uwan mu dake cikin ko wane qangi da masifa na rayuwa, Allah ka kawo masu sauqin shi, Wadanda s**a rigamu zuwa gidan gaskiya Allah ka yi masu rahama. Amin👏🏻👏🏻👏🏻
Allah mutanen mu dake jihohin Sokoto, da kuma na Zamfara, Katsina, Niger, da kuma Kaduna, kafimu sanin tashin hankalin da suke ciki Allah kayi musu maganin shi, mu kuma ka qara tsare mu, ka yalwantar da zaman lafiya a qasarmu baki daya. Amin👏🏻👏🏻👏🏻
Allah duk wanda yake a hannun masu garkuwa da mutane, Allah ka kubutar dashi cikin lafiya da aminci, Masu yi kuma idan har suna da niyyar bari Allah ka basu ikon tuba. Amin👏🏻👏🏻👏🏻
Allah duk buqatocin mu na alkhairi ka fimu saninsu, Allah ka cika mana su domin kai ne Kareemun kuma Raheemun. Amin ya Allah👏🏻👏🏻👏🏻
daga tsangayar masoya mai girma Babban Mataimaki na musamman ga Mai Girma Gwamna akan kimantawa da saka idanu akan dukkanin ayyuka da al’amuran Gwamnatin Jihar Kano, Honorabul Farouk Sule Garo.