09/06/2020
"Duniya, rawar 'yanmata na gaba ya koma baya."ππ
Allah cikin ikonsa karkashin jagoranci Dr. Mustapha Abba Geidam Permanent secretary ministry of Transport and Energy Yobe State,
Yasamu gaggarumar nasarar na zawarcin dawo da shahararran dantakarar nan Wanda ya tsaya takara karkashin jam'iyar People Democratic party (PDP) A shekarar 2019, acikin garin Potiskum, wato HON. ALHAJI AYUBA ADAMU (AYACO),
Madallah da irin wannan babban kamun da Dr. Mustapha Abba Geidam yayi, Dr. Yamika HON. Alh. Ayuba Adamu (AYACO) a hannun His Excellency Hon. Mai Mal Buni Executive Governor of Yobe State cikin walwala da nishadi da farin ciki, wannan ya tabbatar munada Dr. Geidam baya ROWAR FAGE a siyasarsa,
Maigirma Gwamna beyi kasa agwiwarsaba ya fito yakarbeshi hannu biyu haka yanunawa AYACO Gwamna dagaske yake wajen bunne tsurarun yan adawa da s**a rage bada wasaba, kuma yashigo cikin gida Mai daraja wato jam'iyar APC Mai adalci,
AYACO yasamu damar kebancewa waje nadaban tare da mai girma Gwamna hakan yabashi damar zabda abunda yadameshi yake cimasa tuwo akwaryarsa da dalilan da yasa ya chanja sheka zuwa jam'iyar APC Mai adalci,
Cikin nishadi da fara'a irin na Mai girma, yakarbi kokensa kuma yasha alwashin baza'a barshi abayaba za'a tafi da AYACO kafada da kafada Babu ROWAR FAGE insha Allah, bayan kammala tattaunawarsu Gwamna yayi abunda yasabayi na Alkhairi,
Sakamakon Adalcin shugabancin Mai mala na kokarin bunne/shafe jam'iyun adawa acikin jaharnan musamman a zone B. Dubaga iren iren aiyukan cigaba dake kokarin shamfidawa Al'ummarsa misali:
1. Bunkasa harkar Ilimi Mai zurfi da marar zurfi,
2. Kiwon lafiya, Burni da kauyuka lungu da sako,
3. Harkar noma, samarda takin zamani ga manoma da noman rani harma da noman shinkafa acikin jaharnan,
4. Al'adu da wassanni,
5. Harkar shari'a, Babu danniya ko zalinci,
6. Harkokin mata,
7. Harkar tattalin da cigaban masana'antu,
8. Harkar kula da kananan hukumomi,
9. Kula da walwala da jindadin Al'umma,
10. Harkar zirga zirga da sufuri.
Dade sauransu,
Ayaco Yana godiya wa Allah subhanahu wata'ala da yabashi damar dawowa wannan jam'iyar Mai adalci yabar jam'iyar da sukecin dunduniyar junansu, Yana Kara godiya wa Mai girma gwamna da Dr. Mustapha Abba Geidam jagora nagari dodon masu rowar fage, Allah yakara daraja da daukaka da nisan kwana,
Allah yakarawa maigirma gwamna lafiya, yabashi damar aiwatar da aiyukan Alkhairi dayasa agabansa, Ameeeeen.
βοΈβοΈUsman Alhaji Shehu Potiskum.
MMMVG
Mai Mala Media Veterans Group
09/06/2020
Time:08:59pm