Albani Grassroot Mobilization AGM

Albani Grassroot Mobilization AGM Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Albani Grassroot Mobilization AGM, Political organisation, Samaru.

HONOURABLE ADAMU ADAMU MATAZU (JAGORAN GAMAYYAR ƘUNGIYOYIN MATASAN AREWACIN NAJERIYA) YA ZIYARCI DAN TAKARAR SHUGABAN KA...
15/10/2024

HONOURABLE ADAMU ADAMU MATAZU (JAGORAN GAMAYYAR ƘUNGIYOYIN MATASAN AREWACIN NAJERIYA) YA ZIYARCI DAN TAKARAR SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR SABON GARI HON. SHEIKH JAMILU ABUBAKAR ALBANI TARE DA TAWAGAR SA KUMA SUN TABBATAR DA GOYON BAYAN SU A GARE SHI.

A daren Lahadin ta gabata Shugaban gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewacin Najeriya, kuma haifaffen garin Samarun Sabon Garin, Zaria Hon. Adamu Adamu Matazu ya ziyarci dan takarar shugaban karamar hukumar Sabon Gari Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani tare da tawagar sa domin mara masa baya bisa takarar shugaban karamar hukumar Sabon Gari da yake yi.

Hon. Adamu Adamu Matazu a bayanin sa ya bayyana cewa ya kawo wannan ziyara ne tare da jama'arsa domin su nuna goyon baya ga Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani a bisa wannan takarar da yake yi na Shugaban karamar hukumar Sabon Gari. Ya kara da cewa sun duba sunga a kaf cikin yan takarkarin ba wanda yafi shi cancanta, kuma a damammakin da ya samu a baya na shugabanci yayi iya bakin kokarin sa gurin taimakon jama'a da ciyar da yankin mu gaba. Saboda haka ne ya ga ya dace a mara masa baya domin samun cigaban al'ummar mu da yankin mu baki daya.

Daga bisani, Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani yayi godiya kuma ya nuna farin cikinsa ga wannan goyon baya tare da tabbatar da cewa In Sha Allah idan Allah ya bada wannan dama zasu yi duk iya abinda zasu iya don ciyar da wannan yanki namu gaba.

Taron ya samu halartar dimbin matasa daga sassa daban-daban, da Shuwagabannin addini da masu sarauta da sauran su.

Muna Addu'a Allah ya bama Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani Naasara a wannan zaɓe da muke fuskanta ya kuma musu jagora.
Ameen.

Umar Ahmad Abu Mus'ab
SABON_GARI_FIRST

HONOURABLE SHEIKH JAMILU ABUBAKAR ALBANI 100 DAYS IN OFFICE, DAYS WORTHY OF CELEBRATION AND MOTIVATION.Within 100 days i...
23/09/2023

HONOURABLE SHEIKH JAMILU ABUBAKAR ALBANI 100 DAYS IN OFFICE, DAYS WORTHY OF CELEBRATION AND MOTIVATION.

Within 100 days in office Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani Member representing the good people of Basawa Constituency (Deputy Chief Whip Kaduna State House of Assembly and Chairman Committee on Interfaith and Religious Affairs) was able to shows his capacity by providing positive impact to his constituents in the areas of education, Empowerment and more.

In his 100 days in office Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani Samaru Zaria was able to support less privilege students with scholarship within his constituency, Empowered many petty traders, Distributed Fertilizer to Farmers, Payed school fees for students of Islamic Schools, Payed Medical bills of some less privileges among many other important activities and services.

From what we saw in the first 100 days we are optimistic that many good things are coming for the benefit of the Constituents.

We pray that Almighty Allah will continue to guide him and encourage him towards his duties to provide and bring more benefits to the people he is representing.

Umar Ahmad Abu Mus'ab
Concern Constituent.

Jama'ar Basawa Constituency Dan Allah ku fito muyi Senator Uba Sani  da Sheikh Jamilu Abubakar Sheikh Jamil Albani Samar...
27/02/2023

Jama'ar Basawa Constituency Dan Allah ku fito muyi Senator Uba Sani da Sheikh Jamilu Abubakar Sheikh Jamil Albani Samaru Zaria domin cigaban jahar mu da yankin mu.
Waɗan nan bayin Allah da kuke gani sunyi mun gani.

SAKON GODIYA DA BANGAJIYA DAGA ƘUNGIYAR ALBANI GRASSROOTS MOBILIZATION (AGM).A madadin wannan ƙungiya mai Albarka Albani...
19/11/2022

SAKON GODIYA DA BANGAJIYA DAGA ƘUNGIYAR ALBANI GRASSROOTS MOBILIZATION (AGM).

A madadin wannan ƙungiya mai Albarka Albani Grassroot Mobilization (AGM) ƙarƙashin jagorancin Hon.Hamisu Goma Jibrin (Jarman Samaru) da sauran jagororin ƙungiyar na farin cikin mika godiya na musamman ga dukkan masoya da s**a samu halartar taron da ƙungiyar ta gudanar yau a gundumar Jama'a.

Godiya na musamman ga Sheikh Jamilu Abubakar Albani da tawagarsa, Shuwagabannin jam'iyya, da sauran dukkan yan uwa da abokan arziki da s**a samu halartar wannan taro mai albarka..

Alkiblar tafiyar itace APC daga sama har kasa.
Allah ya bamu Nasara ameen.

Directorate of Media and Publicity
Albani Grassroot Mobilization (AGM)
18th November,2022.

*SHUGABANCIN ƘUNGIYAR ALBANI GRASSROOT MOBILIZATION (AGM) TAKAI ZIYARAR GIRMAMAWA TA MUSAMMAN GA HON. MUSTAPHA SHEIKH AB...
25/09/2022

*SHUGABANCIN ƘUNGIYAR ALBANI GRASSROOT MOBILIZATION (AGM) TAKAI ZIYARAR GIRMAMAWA TA MUSAMMAN GA HON. MUSTAPHA SHEIKH ABDALLAH.*

A daren jiya Asabar 24 ga watan September jagorancin ƙungiyar Albani Grassroot Mobilization (AGM) ƙarƙashin jagorancin Hon.Hamisu Jaraman Samaru (Wanda Hon. Mustapha Milgoma ya wakilta) da sauran jagororin ƙungiyar sun kaima Hon. Mustapha Sheikh Abdallah ziyarar girmamawa a garin samaru.

Shugaban ƙungiyar wanda Hon. Mustapha Milgoma ke wakilta tare da mataimakin magatakardar ƙungiyar Hon. Hussaini Muhammad Gamawa sunyi cikakken bayani na abinda ƙungiyar ta ƙunsa tare da ayyukan da ƙungiyar keda kudirin aiwatar wa. Bayan haka shuwagabannin kungiyar sun nemi gudunmawa tare da goyon baya akan ƙudurorin wannan ƙungiya mai Albarka.

Daga bisani Hon. Mustapha Sheikh Abdallah ya nuna farin cikinsa da jin dadi na Ziyarar da aka kawo masa, tare da jinjina ga irin tsare-tsare masu kyau da wannan ƙungiya take dashi kuma ya tabbatar da bada gudunmawar sa a duk lokacin da aka buƙace sa. Bayan haka ya bada shawarwari musu mahimmanci domin samun nasarar dan takarar mu Sheikh Jamilu Abubakar Albani da sauran yan takarkarin Jam'iyyar APC daga sama har kasa.

Taron ya samu halartar Shugabannin kungiyar AGM daga dukkan gundumomi guda huɗu na Basawa Constituency.

Allah ya bamu Nasara ameen.

*Directorate of Media and Publicity,*
*Albani Grassroot Mobilization (AGM)*
*25th September,2022.*

SHUGABANCIN ƘUNGIYAR ALBANI GRASSROOT MOBILIZATION (AGM) TAKAI ZIYARAR GIRMAMAWA GA WASU DAGA CIKIN JAGORORIN JAM'IYYAR ...
12/09/2022

SHUGABANCIN ƘUNGIYAR ALBANI GRASSROOT MOBILIZATION (AGM) TAKAI ZIYARAR GIRMAMAWA GA WASU DAGA CIKIN JAGORORIN JAM'IYYAR APC TARE DA KAI GAISUWAR TA'AZIYYA DA DUBIYAR RASHIN LAFIYA.

A yammacin jiya Lahadi 11 ga watan September jagorancin ƙungiyar Albani Grassroot Mobilization (AGM) ƙarƙashin jagorancin Hon.Hamisu Jaraman Samaru da sauran jagororin ƙungiyar sun kaima Hon.Aliyu Ahmad Manchester da Hon.Shehu Namadi ziyarar girmamawa wanda daga bisani jagorancin ƙungiyar ta kai ziyarar ta'aziyyah da dubiyar rashin lafiya a garin samaru.

Shugaban ƙungiyar Hon. Jarma tare da mataimakin magatakardar ƙungiyar Hussaini Muhammad Gamawa sunyi cikakken bayani na abinda ƙungiyar ta ƙunsa tare da ayyukan da ƙungiyar keda kudirin aiwatar wa. Bayan haka Mai girma Sarkin Zurun Zazzau Alh. Mani Usman ya nemi gudunmawa tare da goyon bayan su akan ƙudurorin wannan ƙungiya mai Albarka.

Daga bisani Hon.Aliyu Ahmad Manchester da Hon.Shehu Namadi sun nuna farin cikinsu da jin dadi na irin tsare-tsare masu kyau da wannan ƙungiya take dashi kuma sun tabbatar da bada gudunmawar su a duk lokacin da aka buƙace su.Bayan haka sun bada shawarwari musu kyau da mahimmanci domin samun nasarar dan takarar mu Sheikh Jamilu Abubakar Albani da sauran yan takarkarin Jam'iyyar APC daga sama har kasa.

Bayan haka Shugaban ƙungiyar ya jagoranci tawagar zuwa ta'aziyyah da dubiyar rashin lafiya a layin Ƴar Tsamiya dake gundumar Samaru.

Taron ya samu halartar Shugaban ƙungiyar Hon.Hamisu Jarma,Mai Girma Wakilin Zurun Zazzau,Hon.Ilyasu Mustapha Basawa, Hussaini Muhammad Gamawa, Women leader AGM da sauran jagorori na tafiyar AGM.

Allah ya bamu Nasara ameen.

Naku a har kullum,
Umar Ahmad Abu Mus'ab
Director Media and Publicity
Albani Grassroot Mobilization (AGM)
12th September,2022.

*ALBANI GRASSROOT MOBILIZATION (AGM) TA ƘADDAMAR DA SHUWAGABANNIN GUNDUMOMI HUDU DAKE BASAWA CONSTITUENCY.*Shuwagabannin...
04/09/2022

*ALBANI GRASSROOT MOBILIZATION (AGM) TA ƘADDAMAR DA SHUWAGABANNIN GUNDUMOMI HUDU DAKE BASAWA CONSTITUENCY.*

Shuwagabannin Albani Grassroot Mobilization (AGM) ta kaddamar tare da rantsar da shuwagabannin gundumomi hudu dake Basawa Constituency.

Gundumar Basawa da Jama'a and ƙaddamar dasu a Jiya Asabar, yau kuma aka ƙaddamar da shuwagabannin gundumar Bomo da Samaru ko wanne a gundumomin su.

Taron kaddamarwar ta samu halartar shuwagabannin AGM, Iyayen Jam'iyaya na yankin Gundumar Basawa, Yan Jam'iyyah da Sauran masoya dan Majalisar gundumar Basawa mai jiran gado Sheikh Hon. Jamilu Abubakar Albani.

Alokacin ƙaddamarwar shuwagabanni sunyi kira ga wadanda aka ƙaddamar dasu jajirce gurin sauke wannan nauyi da ake daura musu don samun nasara.

Shugabannin ƙungiyar na mika godiya ta musamman ga dukkan wanda s**a bada gudummawar su domin nasaran tarurrukan das**a gabata.

Daga naku,
Umar Ahmad Abu Mus'ab
Director Media and Publicity
Albani Grassroot Mobilization.

*ALBANI GRASSROOT MOBILIZATION (AGM) INAUGURATE WARD STRUCTURE WITHIN THE FOUR WARDS OF THE CONSTITUENCY.*The leadership...
04/09/2022

*ALBANI GRASSROOT MOBILIZATION (AGM) INAUGURATE WARD STRUCTURE WITHIN THE FOUR WARDS OF THE CONSTITUENCY.*

The leadership of the Albani Grassroot Mobilization has inaugurated it's ward structure from the entire four wards of the Basawa Constituency.

The Basawa and Jama'a ward structure was inaugurated yesterday Saturday 3rd September,2022 and today Sunday 4th September,2022 the Bomo and Samaru ward structure where inaugurated respectively at their various wards.

The inauguration has in attendance the AGM Central structure, Party stakeholders within the Constituency, party members and other respected supporters of our awaiting member representing the good people of Basawa Constituency Sheikh Hon. Jamilu Abubakar Albani.

During the inauguration the leadership of the ward structures where called upon to be very active and dedicated to the assignment bestowed upon them.
The central structure of the AGM appreciates everyone for their support and contribution to the success of the program.

Yours sincerely.
Umar Ahmad Abu Mus'ab
Director Media and Publicity
Albani Grassroot Mobilization.

01/08/2022

Address

Samaru

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Albani Grassroot Mobilization AGM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share