17/11/2018
KANO
★
★
★
Gari ne mai dumbum tarihi wanda ake alfahari da shi a najeriya da ma Afirika baki daya.
Yana na daga cikin darajojin garin ta irin abubuwan tarihi da garin ya tara.
Tin lokacin Soji ake Gwabnoni iri-iri ko da yadda yake salon milkinsa, Sai gashi mun tsinci kai a hannu miyagun mutane marasa kishin al'umma kuma marasa kishin garin.
Misali, duk wanda yawan Kano da tarihinn Kano yasan Ginin katangar Fadala, a yau sai gashi Gwabnati tana yankawa tana siyarwa.
★
★
★
Illolin da wannan Gwabnati tai a Kano tana da yawa, sai zuwa nan gaba za'a gane hakikanin zaluncin da rashin tsarin hakan.
A Kano an kwacewa mutane runfuna a kasuwa anyi shaguna, an datse hanya anyi Gine-ginen Shaguna, an yanki Makaranta da duk wasu gurare dake karawa garin nan martaba an siyar, an saida Masallacin Idi an sai da Sitadiyam kai har Makabarta an yanka an siyar.
★
Duk da wannan badakala sai kagashi Allah ya nuna mana a zahiri cewa Mutanen nan azzalumai ne, Bazarayi ne mugwaye ne kuma Yan ci da addini ne.
Duba da yadda Siyasa ta matso kusa ya kamata musan wa zamu tsaba, domin idan ka tsabi wannan Gwabnan a karo na biyu baka da hujja da zaka bayar gaban Allah.
Allah yai mana zabi da chanji na kwarai.