Wambai Solidarity Forum 2027

Wambai Solidarity Forum 2027 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Wambai Solidarity Forum 2027, Political organisation, Faskari, Wuse II.

INJI WANI MAI ZABE DAGA FASKARI 1. Cikawa aka fika ba yawan alkawari ba..2. Yaudara gaba kuka ba ta ba baya ba.. 3. Musa...
31/07/2026

INJI WANI MAI ZABE DAGA FASKARI

1. Cikawa aka fika ba yawan alkawari ba..
2. Yaudara gaba kuka ba ta ba baya ba..
3. Musa a baki Fir'auna a zuci..
4. Magana s**a fika ba zaman majalisa ba..
5. Kura ga tsoro ga ban tsoro..
6. Jajirtacce amma awajen wakiltar kai..
7. Aiki aka fiku ba yawan yara ba..
8. Zance 100 ƙarya 99..
9. Dattaku aka fika ba yawan shekaru ba..
10. Inuwar giginya na nesa ka sha ki..

Dan ba ƙara wankan soda, Allah ya raba yari da ɓarawo.. 🏃🏃🏃
Halin wani dan takarar mu da zamu dawo dashi gida insha Allah

Mu kwana lfy

INJI: Wani Mai Zabe Daga Faskari.Ina so kasani  Nifa D S Babu abinda zaiyi ya birgeni Shekara 15 ba amo ba labarin shi y...
29/07/2026

INJI: Wani Mai Zabe Daga Faskari.

Ina so kasani
Nifa D S Babu abinda zaiyi ya birgeni

Shekara 15 ba amo ba labarin shi yo in zaku fadamai cewa kan mage yawaye ku fada mashi

Kuma karubuta ka aje insha allahu hakin maigora ward kade sai ya kada shi don Allah karubuta ka aje

Da izinin Allah
Sai ya girbi abinda ya shuka mudai bazamu yafe mashi rukon sakainar da yayi mana ba kuma hakinmu sai k**a shi

Ya yaudare mu kuma yaci amanar mu don haka bazamu yafe ba don Allah ku fada mashi wannan Sako nawa.

ME: WAMBAI LOKACI YAYI INSHA ALLAH.

INJI ABUBAKAR HAMISU FASKARI Nasarar Jam'iyar mu Ta APC A yankin mu Nada Alaka Da Tsayuwar ka Tsayin daka Wajan Shiga Ci...
28/07/2026

INJI ABUBAKAR HAMISU FASKARI

Nasarar Jam'iyar mu Ta APC A yankin mu Nada Alaka Da Tsayuwar ka Tsayin daka Wajan Shiga Cikin Lamuran Al'umma Hon Hamza Sulaiman Da yawansu da sun san yadda zaka kasance gobe, da ba su yi maka abin da s**a yi maka a yau ba. Ba su san me ake kira “gobe” ba.

Saboda haka, ka kyautata mu'amalarka da kowa, ka zauna da mutane lafiya, tsakaninka da Allah, in sha Allah alheri ne zai biyo baya.

Hon Hamza Sulaiman Faskari Da yawansu da sun san yadda zaka kasance gobe, da ba su yi maka abin da s**a yi maka a yau ba. Ba su san me ake kira “gobe” ba

Hon Hamza Sulaiman Faskari Gobe ta Allah ce, ubangiji Allah zai baka nasara a Wannnan zabe dake tafe

HON. HAMZA SULAIMAN FASKARI, WAMBAN FASKARI, SADAUKIN ƘASAR HAUSA IRayuwar Jagora Mai Kishin Jama'a da Ci Gaban Al'ummaD...
07/07/2026

HON. HAMZA SULAIMAN FASKARI, WAMBAN FASKARI, SADAUKIN ƘASAR HAUSA I

Rayuwar Jagora Mai Kishin Jama'a da Ci Gaban Al'umma

Daga: Saidu Almu Munhaye
07/07/2026.


A tarihin al'ummomi, akan samu mutane kaɗan waɗanda Allah ke yi wa baiwar shugabanci, hangen nesa da kuma son hidimtawa jama'a ba tare da nuna gajiyawa ba. Irin waɗannan mutane su ne ke zama fitilu masu haskaka tafarkin ci gaba, suna barin tarihi mai ɗorewa a zukatan al'umma. Daya daga cikin irin waɗannan jagorori shi ne Hon. Hamza Sulaiman Faskari, wanda aka fi sani da Wamban Faskari kuma Sadaukin Ƙasar Hausa

An haifi Hon. Hamza Sulaiman Faskari a garin Faskari da ke Jihar Katsina, cikin gida mai cike da tarbiyya, ilimi da hidimar jama'a. Mahaifinsa, marigayi Alhaji Sulen-Sule Faskari, ya yi fice a matsayin manomi, ɗan kasuwa, ɗan siyasa kuma mai taimakon al'umma, yayin da mahaifiyarsa, Hajiya Ruqayya, ta shahara da kyawawan ɗabi'u da tarbiyyar addini. Tun yana ƙarami ya fara karatun Alƙur'ani, kafin daga bisani ya shiga makarantun boko domin neman ilimin zamani.

Kishinsa ga ilimi ya sa ya samu digirin farko na Bachelor of Arts (History) daga Jami'ar Bayero Kano a shekarar 2004, sannan ya ƙara samun digirin Master of Public Policy and Administration daga wannan jami'a a shekarar 2008. Baya ga haka, ya halarci ƙarin horaswa a fannin kwamfuta da sauran shirye-shiryen ƙwarewa, yana mai tabbatar da cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaba.

Bayan kammala karatu, Hon. Hamza ya fara aiki a Hukumar Federal Character Commission a shekarar 2009. Daga baya, a shekarar 2011, aka naɗa shi Mataimaki na Musamman ga Sanata Abu Ibrahim a Majalisar Dokoki ta Ƙasa. Waɗannan muk**ai sun ba shi damar ƙara fahimtar shugabanci, gudanar da mulki da kuma hidimar jama'a.

A harkokin siyasa kuwa, Hon. Hamza ya zama ɗaya daga cikin fitattun jagororin APC a Jihar Katsina. Saboda ƙwarewa, jajircewa da amana, Gwamna Aminu Bello Masari ya naɗa shi Kwamishinan Muhalli a shekarar 2015, sannan aka sake ba shi wannan amanar a wa'adi na biyu. Ya ci gaba da riƙe manyan muk**ai a gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufofin ci gaban jihar.

Sai dai abin da ya fi sa sunansa ya yi armashi shi ne ayyukan jin ƙai da yake gudanarwa. Ya taimaka wajen inganta cibiyoyin lafiya, samar da ruwan sha, tallafa wa marasa lafiya, ɗalibai, marayu, mata da matasa, tare da shirye-shiryen koyar da sana'o'i da ba da jari domin dogaro da kai. Haka kuma ya ba da gudummawa wajen kare muhalli da magance matsalolin ambaliya da zaizayar ƙasa a sassa daban-daban na Jihar Katsina.

Irin wannan sadaukarwa ce ta sa aka naɗa shi Wamban Faskari, sannan daga bisani Mai Martaba Sarkin Daura ya ba shi sarautar Sadaukin Ƙasar Hausa I, sarauta mai ɗimbin tarihi da martaba, domin girmama irin gudummawar da yake bayarwa ga al'umma da ƙasar Hausa baki ɗaya.

A yau, Hon. Hamza Sulaiman Faskari yana ci gaba da zama abin koyi ga matasa da shugabanni. Ana kallonsa a matsayin jagora mai hangen nesa, mai son haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban al'umma. Wannan ne ya sa magoya bayansa da dama suke bayyana cewa zai iya wakiltar muradun al'ummar Kankara, Faskari da Sabuwa yadda ya k**ata a Majalisar Wakilai ta Tarayya idan aka ba shi dama. An kuma ruwaito cewa shugabannin APC a yankin sun amince da shi a matsayin ɗan takarar sulhu na mazabar gabanin zaɓen 2027.

Hon. Hamza Sulaiman Faskari ya tabbatar da cewa shugabanci ba magana ba ne kawai, aiki ne, amana ce, da sadaukarwa. Tarihinsa ya nuna cewa ci gaban al'umma yana samuwa ne idan shugaba ya fifita bukatun jama'a fiye da nasa.
"Jagora nagari shi ne wanda tarihinsa ke rayuwa a cikin zukatan al'umma saboda ayyukan alheri da ya bari."

GOBEN ZATA FI YAU DIN KYAU INSHA ALLAH.

Address

Faskari
Wuse Ii

Telephone

+2349150234726

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Wambai Solidarity Forum 2027 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share