20/12/2025
Tabbas Tsarki ya Tabbata Ga Allah
Kuma Haƙiƙa dukkanin wanda ya ba wa Allah rance to sai ya ninka masa ninkin ba ninkin.
A jiya ne da daddare wajen Karatun Dr. Muhammad Aliyu ( Imam Low-Cost ) wanda yake gudanarwa duk ranar juma'a tsakanin magrib zuwa isha'i, bayan angama karatu, to dama mutane na aeko da sadaka don cigaba da aikin Allah, kawai sai wata baiwar Allah ta aiko da taimakon naira #200 tace ayi mata addu'a zata aurar da ɗiyarta nan da wata daya amma basu da halin yin kayan daki, tanaso Malam yayi mata addu'a Allah ya basu mafita.
Ae ko nan take Allah ya amsa addu'an ta, domin dama shi maji rokon bawa ne, sai Allah yasa Jarman Zazzau Alhaji Muktar ibrahim yaji koken matan, ae ko nan take yace, asanar da matan da ta aiko da waliyanta agaya masa abunda za'a kashe a kayan dakin yarinyar nata, ya dauki nauyin yi mata kayan. Abun lura anan shine matan ta bawa Allah rance nan take kuma Allah ya nuna shi Allah ne.
Don haka jama'a wallahi mukara dagewa da sadaka da taimakon wanda basu dashi. Muna rokon Allah S.W.A ya saka mishi da alkhairii, ya ubangiji kaman yanda wannan bawa naka ya taimaki wannan bayin naka, Allah ka cika masa burikan shi na alkhairi, Allah ka tsare gabanshi da bayanshi, ya Allah ka kara kawo mana irinsa acikin al'uman musulmai.
Kasar Zazzau a Jiya Da Yau