MUAZU Muhammad SHEHU ZURMI

MUAZU Muhammad SHEHU ZURMI STUDYING AT FEDERAL UNIVERSITY GUSAU

10/05/2021

ONAGODIYA GA MUTANAN GIDAN NAN ALLAH YASAKAMAKU DA ALKHAORIN SA AMEEN

21/12/2020
11/11/2020

An zabi mutanen da zasu ci moriyar shirin a wannan daga jihohi goma da ke sassa daban-daban na Najeriya

A yayin da batagarin mutane ke tsaka da cigaba da barna a sassan kasa, gwamnatin tarayya ta sanar da kaddamar da shirin bunkasa tattalin arziki.

A karkashin wannan shiri, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta fara biyan N30,000 ga masu sana'ar hannu.

A cewar gwamnatin tarayya, za ta biya kudin sau daya ga kowanne mutum.

Kudin da aka fara rabawa na daga cikin kudaden da aka ware domin farfado da kananan masana'antu da bullar annobar korona ta kassara.

An fara biyan kudaden ne zuwa asusun masu sana'ar hannu da aka tantance a jihohi goma.

Jihohi 10 da aka zaba a matsayin rukuni na farko domin fara biyan mutanensu sun hada da; Abuja, Lagos, Kaduna, Ondo, Kano, Borno, Abia, Bauchi, Anambra, Ribas, Filato, da Delta.

Mutanen da aka zaba daga jihohin sun aika bayanansu tsakanin 1 ga watan Oktoba zuwa ranar 10 ga wata ta shafin yanar gizo da aka bude domin neman tallafin.

Masu kananan sana'o'i
Source: Original

Shugaba Buhari ne ya kaddamar da shirin bawa kananan masana'antu tallafi (MSMEs Survival Fund) a cikin watan Maris, 2020.

Shirin ya na daga cikin babban tsarin raya tattalin arziki (NESP) wanda shugaba Buhari ya nada mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a matsayin jagora.

A saboda haka, ofishin Osinbajo ne zai sa ido a kan kaddamar da shirin tare da tafiyar da komai bisa manufofi da ka'idojin da gwamnati ta gindaya.

An tura masu yi wa jama'a rijistar zuwa sauran jihohin da za a bayar da tallafin a sauran rukunai da zasu biyo baya.

Gwamnati ta shawarci masu sana'o'in hannu su tuntubi shugabannin kungiyoyinsu domin mika sunayensu.

An fara rijistar mutane a rukuni na biyu daga ranar 19 ga watan Oktoba a jihohin Edo, Ogun, Ekiti, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Enugu, Ebonyi, Adamawa, Taraba, da Bayelsa.

A bangare guda, har yanzu ana cigaba da tantance bayanai da takardun wadanda s**a nemi tallafi a karkashin tsarin biya masu matsakaitan masana'antu.

Sai dai

07/11/2020

Bayanan hoto, Tun da farko Rahama Sadau ta nemi afuwa cikin kuka kan ɓatancin da aka yi wa Musulunci kan hotunanta

Fitacciyar jaruma Kannywood Rahama Sadau ta ce ta zama abin tausayi kan hotunan da ta saka da s**a janyo cin mutuncin addininta.

Jarumar wadda tun a farko ta ce ta yi nadamar wallafa hotunan, ta shaida wa BBC cewa ta ji zafin yadda 'yan Kannywood suke maganganu kan lamarin, wanda ta ce ya faru ba tare da san ranta ba.

A ranar Litinin ne sunan Rahama Sadau ya fara waɗari a Twitter, inda aka ambaci sunan sau fiye da 10,000, bayan hotunan da ta tauraruwar ta saka s**a ja hankalin masu bibiyarta da kuma masu amfani da Twitter musamman daga arewaci da kudancin Najeriya.

Hotunan jarumar sun haifar da mahawara tsakanin masu amfani da kafofin sadarwa, lamarin da har ya kai ga yin kalaman ɓatanci Annabi Muhammadu SAW.

Jarumar ta bayyana cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram sanye da hijabi, cikin kuka da murya mai rawa, tana neman a yafe mata.

A hirarta da BBC kuma ta ce duk wani mai hankali idan ya zauna ya kalli abin da ya faru zai gane cewa ta zama abin abin tausayi.

"Wani ya kamata ya yi tunanin shin ya Rahama take ji a matsayinta na musalma," in ji ta.

Ta ce da dare ta saka hotunan ta tafi ta yi bacci, ba tare da ta tsaya diba me ake cewa ba game da hotunan da ta wallafa.

"Sai da safe ina tashi na ga tsokaci dubu 10, ban san me ke faruwa ba. A haka wani ya turo min da sako na ɓatancin da aka yi. Ina ganin wannan na san cewa saka hoto ya koma wani abu"

Rahama Sadau: Ba da yawuna aka ci zarafin Musulunci ba a Twitter

Rahama Sadau ta nemi afuwa cikin kuka kan ɓatancin da aka yi wa Musulunci kan hotunanta

Game da martani daga abokan sana'arta 'yan Kannywood, Rahama ta ce su ya kamata su fara ankarar da ita. "Amma kila waɗanda suke maganar sun riga ni gani amma ba za su iya kira na ba, gara su bari a yi ta magana akai"

Jarumar ta ce idan da tsokacin mutane ne kawai ba za ta damu ba. Amma ta ce yin ɓatanci ga Annabi SAW ya girgiza t

03/11/2020

Shugaban Buhari ya ce sama da mutum miliyan ɗaya ne s**a cike tallafin NYIF tun bayan bude shafin cike tallafin a yanar gizo ranar 12 ga watan Oktoba, 2020.

- Buhari ya ƙara da cewa ba wannan ne karon farko da gwamnatinsa ta ƙirƙiri dama irin wannan ga matasa ba

- A cewar Buhari, gwamnatinsa ta ƙirƙiri tsare-tsare sama da 25 don cigaban matasa

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari yace sama da mutane miliyan ɗaya ne s**a cike tallafin sana'o'i na matasa(NYIF)cikin sati uku da buɗe cike tallafin tun 12 ga watan Oktoba,2020.

Buhari,wanda ministan tarayyar Muhammad Bello ya wakilta,ya bayyana saƙon a ranar murnar matasa a ranar Lahadi.

Tallafin NYIF, wanda ya samu sahalewa daga hukumomin tarayya (FEC) a ranar 22 ga watan Yuli, 2020, an yi shine don tallafawa mutane masu karanchin shekaru; daga shekara 18 zuwa 35, kuma zai kai tsawon shekaru uku (2020-2023).

"Wannan kuɗaɗe an waresu musamman don zuba jari a tunani, fikira da fasahar matasan Najeriya domin basu damar kasuwanci, da abubuwan da ake buƙata don ƙirƙirar sana'o'i.

"Sama da mutane miliyan ɗaya s**a samu damar cike tallafin tun bayan buɗe shafin yanar gizo na tallafin NYIF a ranar 12 ga watan Oktoba 2020", a cewarsa.

Buhari ya bayyana matasa a matsayin masu kawo sauyi a ƙasa a ɓangarorin zamantakewa, ɓunkasa tattalin arziƙi, da kuma samun cigaba mai ɗorewa.

Buhari da shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya
Source: UGC

Buhari yace gwamnatinsa ta ƙirƙiri tsare-tsare sama da 25 musamman don inganta rayuwar matasa a faɗin ƙasa.

A cewar Buhari, tsare-tsaren gwamnatinsa don matasa sun haɗar da:

Tsarin cigaban matasan Najeriya (NYP), Nigeria Youth investment fund(NYIF) wanda aka kaddamar a watan Juli 2020,Tsarin DEEL,wanda aka warewa Naira biliyan huɗu ₦4b don gudanarwa.

Sauran sun haɗar da sahalewar dokar bawa matasa damar mulki ( too young to run.), N-power, Tsarin P-YES, Tsarin YES, tsarin YouWIN, tsarin GIS da sauran su.

Buhari ya ƙara da ''cewa matasa sune ƙashin bayan al-umma wanda zasu kai ƙasa ga ci. I

02/11/2020
02/11/2020

Daga Usman Nasidi.

TSOHON mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya kushe kasafin kudin shekara mai zuwa da shugaban kasa ya gabatar a gaban majalisar tarayya.

Alhaji Atiku Abubakar ya ke cewa wasu daga cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta kawo a a kundin kasafin kudin na 2021, sun ci karo da dokokin kasa.

Jagoran adawar kasar ya bukaci shugaban kasar Najeriya da mukarrabansa, su je su sake zama a kan kundin kasafin na badi, da nufin ceto tattalin arzikin kasa.

A ranar Juma’a ne Abubakar ya fitar da wani dogon jawabi da ya yi wa take da: “The 2021 Budget Proposal Contravenes The Fiscal Responsibility Act.”

‘Dan takarar shugaban kasan na PDP a 2019 ya yi kira ga shugaban kasa ya yi wa kundin gyare-gyare, ta yadda kasafin ba zai ci karo da dokar batar da kudi ba.

Haka zalika, Atiku Abubakar ya bukaci ayi wa kasafin kudin kasar kwaskwarima ta yadda za a iya shawo kan matsalar tattalin da ke damun Najeriya a halin yanzu.

“Kasafin ya na da gibin Naira tiriliyan 5.21. Wannan kaso ya kai kusan 3.5% na jimillar tattalin arzikin Najeriya a 2019, hakan ya saba da dokar kudi ta 2007.”

Atiku ya kara da cewa sashe na 12 na wannan doka ya ce bai halatta a samu gibin fiye da 3% na karfin GDP a kasafin kudin da za a gabatar a gaban majalisa ba.

Ya ce: “Najeriya ta na GDP na $447b a 2019. 3% na wannan shi ne $13.3, idan aka yi lissafin Dala a kan N379, wannan adadi zai ba ka Naira Tiriliyan 5.07”

Don haka ne Atiku ya ce gibin da za a samu a kasafin 2021 ya zarce abin da doka ta yi tanadi.

A makon jiya, mun kawo maku dalla-dallar yadda Najeriya za ta batar da kudin kasafin shekara mai zuwa, inda ake sa ran a batar da Naira tiriliyan 13.08.

02/11/2020

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yaba da tsarin shugabanci na Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara…

Address

Zurmi

Telephone

+2347065931024

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MUAZU Muhammad SHEHU ZURMI posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to MUAZU Muhammad SHEHU ZURMI:

Share