Buhari Sallau

Buhari Sallau BSOM is a Non-Profit Socio Political Platform aimed at equipping the average Nigerian's with necessa

Sojoji sun ceto mutane 23, sun hallaka ’yan ta’adda 19 a cikin sa'o'i 24Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto...
08/12/2026

Sojoji sun ceto mutane 23, sun hallaka ’yan ta’adda 19 a cikin sa'o'i 24

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da hallaka ’yan ta’adda 19 a wasu samame da sintiri da aka gudanar a sassan kasar cikin sa’o’i 24 da s**a gabata.

A Zamfara, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 18 da aka yi garkuwa da su a Sabon Gari, karamar hukumar Kaura Namoda, bayan da s**a mayar da martani ga kiran neman agaji, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa. A Jihar Filato kuma, sojoji sun ceto wani mutum da aka sace daga Duguri a Bauchi, yayin da Operation ENDURING PEACE ta hallaka wani dan ta’adda tare da kwato AK-47 da harsasai biyu.

A Kebbi, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun hallaka ’yan ta’adda 18 yayin da s**a kai hari kan jami’an Mobile Police Special Intervention Squad a Makuku, karamar hukumar Sakaba. Sojojin sun kuma lalata babura biyar tare da kwato bindigogi AK-47 guda biyu da aka kera a gida a wani samame a Filato.

A Borno, dakarun Operation HADIN KAI sun ceto mutane biyar da s**a tsere daga wani sansanin ’yan ta’adda a yankin tsaunukan Mandara, bayan rikici ya barke tsakanin ’yan ta’addan. A Enugu kuwa, sojoji sun kwato AK-47 guda hudu, magazin bakwai da harsasan 7.62mm guda 133 daga maboyar masu garkuwa da mutane a dajin Umuchingu Ujenike.

A Taraba, dakarun sun k**a mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka a karamar hukumar Gashaka, tare da kwato babura, injinan famfo, wayoyin hannu da kudade. Rundunar ta ce ayyukan na daga cikin kokarin da take yi na amfani da bayanan sirri, sintiri da samame domin dakile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassan Najeriya.

Nijeriya na buƙatar haɗin kai yanzu fiye da kowane lokaci – Ministan Yaɗa LabaraiMinistan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, ...
08/11/2026

Nijeriya na buƙatar haɗin kai yanzu fiye da kowane lokaci – Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su ɗaukaka tunanin su sama da bambance-bambancen addini, ƙabila da siyasa, su haɗa kai wajen yaƙi da rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar.

Idris ya yi wannan kiran ne a ranar Talata, a wajen taron ƙasa da ƙasa mai taken “Bambance-bambance da Zaman Lafiyar Al'umma: Haɗin Gwiwa don Kyakkyawar Makoma,” wanda ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) ta shirya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (Muslim World League) a Abuja.

Ministan ya ce bambance-bambancen mutanen da s**a halarci taron ya nuna cewa akwai fahimtar juna cewa tsaro, zaman lafiya da wadata a Nijeriya sun dogara ne da yadda 'yan ƙasa za su yi aiki tare ba tare da la'akari da bambance-bambancen addini, ƙabila da siyasa ba.

Idris ya ce: “Dukkan mu muna buƙatar mu haɗa kai, mu yi tunani a matsayin 'yan Nijeriya, mu yi tunani a matsayin 'yan'adam, kuma mu yi aiki tare ba tare da la'akari da bambance-bambancen mu ba, domin mu kasance tsintsiya maɗaurin ki ɗaya.”

Ya jaddada cewa rarrabuwar kawuna bisa addini da ƙabila za ta ƙara dagula yaƙi da rashin tsaro, yana mai kira ga 'yan Nijeriya da su yi watsi da tashin hankali, rashin haƙuri da ƙoƙarin amfani da bambance-bambancen ƙasar nan wajen raba kan al'umma.

“Babu lokacin bambance-bambance. Idan a yayin yaƙin da muke yi da rashin tsaro muka bari bambance-bambancen addini s**a shiga, hakan zai ƙara dagula matsalar. Buƙatar da muke da ita ta haɗa kan mu a matsayin al'umma ɗaya na da matuƙar muhimmanci,” inji shi.

Idris ya fayyace cewa ba Gwamnatin Tarayya ce ta shirya taron ba, sai dai ya ce gwamnati tana maraba da shirye-shiryen da ke inganta tattaunawa tsakanin mabiya addinai, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

“Idan muna son ci gaba da tafiya zuwa ga wadata, dole ne dukkan mu mu yi tunani da aiki tare, mu kuma haɗa kai a matsayin al'umma ɗaya,” inji ministan.

Ya ce yawan al'ummar Nijeriya, muhimmancin ta da kuma tasirin ta na nufin zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasar na da matuƙar tasiri ga Afirka da ma sauran sassan duniya.

“Nijeriya ƙasa ce mai matuƙar muhimmanci. Ƙasa ce mai mutane sama da miliyan 230. Zaman lafiya da kwanciyar hankali a nan na nufin zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk faɗin Afirka, har ma da duniya baki ɗaya,” inji shi.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron, ya isar da saƙon aniyar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da ingantaccen tsaro mai ɗorewa, haɗin kan ƙasa da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, yana mai cewa Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da abokan hulɗar ta na ƙasa da ƙasa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya kuma Shugaban Ƙungiyar Malaman Musulunci ta Duniya, Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, ya buƙaci 'yan Nijeriya da su kare haƙƙin ɗan'adam da s**a yi tarayya a cikin ta, tare da yin watsi da ƙoƙarin amfani da addini, ƙabila ko talauci wajen raba kan ƙasa.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya yi kira da a ci gaba da tattaunawa, tsare gaskiya da ƙara ƙaimi wajen aiwatar da hanyoyin magance ƙalubalen Nijeriya, tare da kira ga 'yan Nijeriya da su sake gina amana da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin mabiya addinai.

A nasa jawabin, Shugaban jam'iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya buƙaci 'yan Nijeriya da su ɗauki bambance-bambancen ƙasar a matsayin tushen ƙarfi maimakon rarrabuwar kai, yana mai cewa duk da cewa 'yan Nijeriya suna gudanar da ibada ta hanyoyi daban-daban, suna da buri da ƙalubale iri ɗaya.

Shugaban JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, ƙungiyoyin addini da al'ummomi wajen yaƙi da rashin tsaro, tare da ƙara zuba jari a fannin ilimi da bunƙasa ƙwarewa domin rage yiwuwar matasa su rungumi tsattsauran ra'ayi ko kuma a ɗauke su aikin laifi.

Daga cikin waɗanda s**a halarci taron akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu; Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani; Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi; Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum; Ministan Bunƙasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III; Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda; Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa; Shugaban JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau; Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), da sauran manyan jami'an gwamnati, shugabannin addinai da na gargajiya, jami'an diflomasiyya, wakilan ƙungiyoyin fararen hula da sauran manyan baƙi.

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kotun Laifukan Talla domin ƙarfafa tsarin gudanar da harkar tallaGwamnatin Tarayya ta ƙ...
08/11/2026

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kotun Laifukan Talla domin ƙarfafa tsarin gudanar da harkar talla

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabuwar Kotun Laifukan Talla, a wani mataki na ƙarfafa tsari da sa ido kan harkar talla, inganta ƙwarewa da tabbatar da bin ƙa'ida a masana'antar talla da sadarwar kasuwanci a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wurin ƙaddamar da kotun a Abuja, yana mai bayyana kafa kotun a matsayin wani muhimmin mataki wajen gina masana'antar talla mai ƙwarewa da ɗaukar nauyi.

Ya ce: “Mu gina masana'antar talla da za ta yi fice wajen ƙirƙire-ƙirƙire, ta samu amincewar jama'a kuma ta kiyaye ɗaukar nauyi."

Ministan ya ce Dokar Majalisar Kula da Harkokin Talla ta Nijeriya (ARCON) mai lamba 23 ta shekarar 2022 ta faɗaɗa ikon hukumar na tsarawa da sa ido kan harkar talla, tare da tanadar da kafa kotun domin sauraron laifukan da s**a shafi dokar da kuma ƙa'idoji da dokokin da s**a shafi harkar talla.

Ya buƙaci sabuwar kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Cecilia M. A. Olatoregun, da ta gudanar da ayyukant ta cikin gaskiya, 'yanci da adalci.

A cewar sa, “Duk wata shari'a da aka gabatar a gaban ku, ku duba ta bisa hujjojin da ke cikin ta, ba tare da tsoro ko nuna son kai ba, ko ƙauna ko ƙiyayya. Dole kotun ta kasance, kuma a gan ta a matsayin hukuma mai adalci da rashin nuna son kai."

Idris ya taya shugabar da sauran membobin kotun murna, tare da tabbatar masu da ci gaba da goyon bayan ma'aikatar ga ARCON da ƙoƙarin gina masana'antar talla da za ta iya yin gogayya a duniya.

Tun da farko, Darakta-Janar na ARCON, Dakta Olalekan Olumuyiwa Fadolapo, ya bayyana ƙaddamar da kotun a matsayin wani babban mataki wajen ƙarfafa tsari da bin ƙa'idoji a masana'antar talla.

“Kotun Laifukan Talla wata babbar dama ce ga masana'antar talla ta Nijeriya. Ita ce irin ta ta farko a duniya, domin Nijeriya ta ɗauki matakin hangen nesa, ba wai kawai wajen kafa dokoki kan harkar talla ba, har ma da samar da tsare-tsare da tsarin gudanarwa,” inji Fadolapo.

Shugabar Kotun Laifukan Talla, Mai Shari'a Cecilia M. A. Olatoregun, ta yi alƙawarin cewa sabuwar kotun za ta gudanar da ayyukan ta cikin gaskiya, adalci da ƙwarewa.

“Babban abin alfahari ne a kira mu domin yi wa ƙasar mu hidima, kuma mun ɗauki wannan nauyi da muhimmanci sosai. An buƙace mu da yin aiki cikin gaskiya, kuma wannan shi ne abin da za mu yi,” inji ta.

Membobin kotun sun haɗa da Musa Ahmed Attah, SAN; Merga Tyowanan Kachina, Esq.; Dakta Ken Onyeali Ikpe, FRPA; da Hajiya Sa’a Ibrahim, RPA.

Daga cikin waɗanda s**a halarci taron akwai Babbar Sakatare ta Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem Ukaire; Darakta mai kula da Sadarwar Jama'a da Wayar da Kai na Ƙasa, Henshaw Ogubike; Daraktan Hulɗa da Jama'a da Ƙa'idojin Gudanarwa, Dakta Suleiman Haruna; da Mataimaki na Musamman kan Harkokin Gudanarwa ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Sunday Baba, da sauran manyan baƙi.

FMINO PRESS RELEASEFG INAUGURATES ADVERTISING OFFENCES TRIBUNAL TO STRENGTHEN INDUSTRY REGULATION, URGES MEMBERS TO SERV...
08/11/2026

FMINO PRESS RELEASE

FG INAUGURATES ADVERTISING OFFENCES TRIBUNAL TO STRENGTHEN INDUSTRY REGULATION, URGES MEMBERS TO SERVE WITH INTEGRITY

The Federal Government has inaugurated the newly constituted Advertising Offences Tribunal as part of efforts to strengthen regulation, promote professionalism and ensure greater integrity in Nigeria’s advertising and marketing communications industry.

The Honourable Minister of Information and National Orientation, Mohammed Idris, stated this on Tuesday at the inauguration of the Tribunal in Abuja, describing the development as an important step towards building a more professional and responsible advertising industry.

“Let us build an advertising industry that commands creativity, earns trust, and upholds responsibility,” Idris said.

The Minister said the Advertising Regulatory Council of Nigeria (ARCON) Act No. 23 of 2022 expanded the Council’s regulatory powers and provided for the establishment of the Tribunal to adjudicate offences under the Act and relevant advertising regulations and codes.

He urged the new panel, led by Honourable Justice Cecilia M. A. Olatoregun, to carry out its duties with integrity, independence and fairness.

“Every matter that comes before you should be considered on its merits, without fear or favour, affection or ill will. The Tribunal must be, and must be seen to be, a fair and impartial institution,” he said.

The Minister congratulated the Chairman and members of the Tribunal, assuring them of the Ministry’s continued support for ARCON and efforts to build a globally competitive advertising industry.

Speaking earlier, the Director-General of the Advertising Regulatory Council of Nigeria (ARCON), Dr. Olalekan Olumuyiwa Fadolapo, described the inauguration of the Advertising Offences Tribunal as a major step in strengthening regulation and compliance in the advertising industry.

“The Advertising Offences Tribunal is a big opportunity for the Nigerian advertising industry. It is the first of its kind in the world because Nigeria has taken a proactive step not only to legislate on advertising, but also to put structures and frameworks in place,” he said.

The Chairman of the Advertising Offences Tribunal, Honourable Justice Cecilia M. A. Olatoregun, pledged that the new panel would discharge its responsibilities with integrity, fairness and professionalism.

“It is a great honour to be called upon to serve our country, and we take this responsibility very seriously. You have asked us to work with integrity, and that is what we are going to do,” she said.

Members of the Tribunal are Musa Ahmed Attah, SAN; Merga Tyowanan Kachina Esq; Dr. Ken Onyeali Ikpe, frpa; and Hajia Sa'a Ibrahim, rpa.

In attendance was the Permanent Secretary of Information and National Orientation, Dr Binyerem Ukaire; the Director, Public Communication and National Orientation, Henshaw Ogubike; the Director, Public Relations and Protocol, Suleiman Haruna, PhD; the Special Assistant (Admin) to the Honourable Minister of Information and National Orientation, Dr Sunday Baba, among other dignitaries.

Rabiu Ibrahim, mnipr
Special Assistant (Media) to the Honourable Minister of Information and National Orientation

Tuesday, 11 August, 2026

MINISTA BAGUDU YA HALARCI TATTAUNAWAR TSARON ƘASA A ABUJAMinistan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubaka...
08/11/2026

MINISTA BAGUDU YA HALARCI TATTAUNAWAR TSARON ƘASA A ABUJA

Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya halarci Taron Ƙasa da Ƙasa kan Tsaron Ƙasa da Muslim World League tare da haɗin gwiwar JIBWIS Nigeria s**a shirya a Abuja.

Taron, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Dr. Muhammad bin Abdulkarim Al-Issa, ya mayar da hankali kan ƙalubalen tsaro da hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin dorewar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a Najeriya.

Taron ya samu halartar manyan shugabanni, malamai, sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati.

08/11/2026
NASENI  Empowers Osun Youths, Women With Advanced Technical Skills, EquipmentThe National Agency for Science and Enginee...
08/11/2026

NASENI Empowers Osun Youths, Women With Advanced Technical Skills, Equipment

The National Agency for Science and Engineering Infrastructure (NASENI) has empowered young people and women in Ile Ife, Osun State, with advanced technical skills and equipment under its NASENI Sustainable Empowerment Programme (NSEP).

This was disclosed in a statement issued on Monday by the NASENI Information unit, stressing that it was aimed at promoting self-reliance, entrepreneurship and sustainable livelihoods.

The three -day training programme, held from August 7 to 9, 2026, at the NASENI Skills Acquisition Centre, Ile Ife, exposed beneficiaries to Advanced Photography and Drone Operations, Advanced Shoemaking, CCTV and Inverter Installations, and Advanced Tailoring, equipping participants with practical knowledge and tools to establish or strengthen income-generating ventures.

Speaking at the closing ceremony, the executive Vice chairman/chief executive Officer of NASENI, Khalil Suleiman Halilu, represented by the overseeing officer, Prototype Engineering Development Institute (PEDI), Ilesha, Ahmed Olaoye Hamzat, said the initiative was designed to move empowerment beyond the presentation of certificates to providing beneficiaries with practical skills, tools and opportunities capable of translating into sustainable livelihoods and economic independence.

He explained that the programme deliberately combined skills acquisition with the provision of relevant equipment to enable beneficiaries to immediately put their knowledge into practice.

The National Agency for Science and Engineering Infrastructure (NASENI) has empowered young people and women in Ile Ife, Osun State, with advanced technical

08/11/2026

Isowar manyan baki a zauren taron Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (Muslim World League) kan tsaro a Abuja.

08/11/2026

Ana gab da fara taron ƙasa da ƙasa na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (Muslim World League) kan tsaro a Abuja.

Manyan baki na cigaba da halara zauren taron na Bola Ahmed Tinibu International Conference Center.

Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya za ta gudanar da taron ƙasa da ƙasa kan tsaro a AbujaƘungiyar Ƙasashen Musulmi ta Du...
08/10/2026

Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya za ta gudanar da taron ƙasa da ƙasa kan tsaro a Abuja
Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (The Muslim World League), tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidiah Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS), za ta gudanar da taron ƙasa da ƙasa kan tsaro a Abuja ranar Talata, da nufin inganta zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da tsaro.

Za a gudanar da taron ne a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu, inda za a haɗa shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna alaƙar da ke tsakanin zaman lafiya, tsaro da cigaban zamantakewa da tattalin arziki.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ƙaddamar da wani sabon masallaci da aka gina a Abuja, wanda Babban Sakatare Janar na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya kuma Shugaban Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci ta Duniya, Sheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-Issa, ya jagoranta.

Idris, wanda tun da farko ya tarbi Sheikh Al-Issa a Ɓangaren Shugaban Ƙasa na Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, tare da raka shi zuwa wurin ƙaddamar da masallacin, ya bayyana ziyarar a matsayin wata shaida ta kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya, Saudiyya da sauran ƙasashen duniya.

Ya ce taron yana zuwa ne a wani muhimmin lokaci da Nijeriya take ci gaba da ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa, tare da aiwatar da sauye-sauye da zuba jari da nufin hanzarta cigaban zamantakewa da tattalin arziki.

Ministan ya sake jaddada aniyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'ummomi, daidaituwar addinai da haɗin kan ƙasa, yana mai cewa zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙan wadata da zaman lafiyar Nijeriya da Afrika.

Idris ya ce: “Shugaban Ƙasa ya ƙudiri aniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba a Nijeriya kaɗai ba, har ma a faɗin duniya. Wannan wata bayyananniyar shaida ce ta hanyar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake bi.”

Ya ce Nijeriya, kasancewar ta ƙasa mafi yawan al'umma a Afrika, tana da babban nauyi da ya rataya a wuyan ta na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin nahiyar, yana mai cewa Nijeriya mai zaman lafiya da tsaro za ta yi tasiri mai kyau a Yammacin Afrika da nahiyar baki ɗaya.

A cewar sa, taron zai samar da wata muhimmiyar kafa da shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki za su yi amfani da ita wajen musayar ra'ayoyi da samar da hanyoyin da za su taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya tsakanin al'ummomi, tsaro da fahimtar juna.

Idris ya yaba wa Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya, JIBWIS, Gwamnatin Saudiyya da sauran masu ruwa da tsaki bisa sauƙaƙa ziyarar Sheikh Al-Issa da kuma kafa masallacin.

Ya yi godiya ga Sheikh Al-Issa bisa ci gaba da jajircewar sa wajen inganta zaman lafiya, tattaunawa da fahimtar juna tsakanin al'ummomin mabiya addinai daban-daban.

Tun da farko, Sheikh Al-Issa ya yaba wa ƙoƙarin Shugaba Tinubu na inganta zaman lafiya tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba, yana mai cewa zaman lafiya da daidaito a Nijeriya za su bayar da gagarumar gudunmawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a Yammacin Afrika da sauran sassan duniya.

Babban Sakatare Janar ɗin ya ce ziyarar sa ta ta'allaƙa ne kan zaman lafiya da zaman lafiya tsakanin al'ummomi, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa taron zai samar da muhimmiyar kafa wajen ciyar da tattaunawa da fahimtar juna gaba a Nijeriya da duniya baki ɗaya.

Ana sa ran taron zai haɗa shugabannin addinai, masu tsara manufofi da sauran masu ruwa da tsaki a wuri guda.

Daga cikin waɗanda s**a tarbi Sheikh Al-Issa a filin jirgin saman akwai Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu Sokoto; Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate; Ministan Ƙwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyaɗi; Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, mai wakiltar Mazaɓar Sanatan Sakkwato ta Arewa; Sanata Mohammed Ɗanjuma Goje, mai wakiltar Mazaɓar Sanatan Gombe ta Tsakiya; Sanata Ahmed Sani Yerima, da sauran manyan baƙi.

Address

610 Madison Avenue, Apt 1
Albany, NY
12208

Telephone

+16463314426

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Buhari Sallau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share