12/23/2025
HOTUNA:
Yadda gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, ya isa garin Kano don halartar bikin kaddamar da hukumar yaฦi da miyagun laifuka da matsalolin tsaro mai suna Kano Neighborhood Watch Corp.
Tabbas Katsina ta zama madubi ga sauran jihohi wajen dabaru da hanyoyin cigaba.
Bayan kafa Katsina Security Watch Corp (C-Watch), duka watanni bayan cin zabe, gwamna Radda ya zama abin koyi ga sauran gwamnoni wanda daga baya Zamfara tayi, Sokoto tayi kuma yanzu ma Kano zatayi.
Tabbas wannan hanya ce dake nuna haษim kai tsakanin gwamnoni don magance matsalar tsaro da kuma inganta rayuwar yankunan mu.
Allah ya bamu zama lafiya da arziฦi mai ษorewa.